1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ministan Tsaron Najeriya ya yi murabus

December 2, 2025

Murabus din na Mohammed Badaru Abubakar ya zo ne a lokacin da kasar ke fama da karuwar matsalar tsaro.

Ministan Tsaron Najeriya Mohammed Badaru Abubakar
Ministan Tsaron Najeriya Mohammed Badaru AbubakarHoto: Nigeria Minister of Defense

Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa a ranar Litinin da dare, a lokacin da kasar ke fuskantar kalubalen tsaro da suka hada da garkuwa da dalibai da dama da dai sauransu.

Fadar shugaban Najeriya ta ce murabus din na zuwa ne mako guda bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokat ta baci kan tsaro, saboda karuwar garkuwa da mutane.

Yawaitar hare-haren Boko Haram a Najeriya

A watan da ya gabata an sace daruruwan mutane galibinsu dalibai a cikin kwanaki kalilan a jihohin Kebbi da Neja da kuma wani hari a coci a jihar Kwara.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa Badaru, mai shekara 63, ya yi murabus ne saboda dalilan lafiya, kuma murabus dinsa ya fara aiki nan take.

Najeriya, wacce ita ce mafi yawan jama’a a Afirka, na fama da matsalolin tsaro da suka hada da garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga da kungiyoyin masu aikata laifuka daban-daban.

Tarayyar Afirka ta ce babu kisan kiyashi a Najeriya

A karshen Oktoba, Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya Najeriya cikin jerin Kasashen da ake Zargi da Tauye ‘Yancin Addini, yana zargin cewa 'yan ta’adda na yi wa Kiristoci kisan kiyashi.