1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ministar raya kasashe masu tasowa ta Jamus ta isa Lebanon

November 4, 2024

Ministar raya kasashe masu tasowa ta Jamus Svenja Schulze ta isa kasar Lebanon domin taron gangamin shigar da kayan agajin jinkai kasar da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Isra'ila da Hezbollah.

Ministar raya kasashe masu tasowa ta Jamus, Svenja Schulze, a yayin tattaunawarta da DW kan yakin Ukraine
Ministar raya kasashe masu tasowa ta Jamus, Svenja Schulze, a yayin tattaunawarta da DW kan yakin UkraineHoto: DW

A watan Oktoban 2023,  majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta amince da bada tallafin karin Euro miliyan 60 kwatankwacin Dalar Amurka miliyan 65.4 domin shigar da kayan agajin jinkai da suka hadar da ruwa da abinci da magunguna ga dubban 'yan gudun hijra da ke jibge a sassa daban daban na Lebanon.

Karin bayani: Jamus za ta bai wa Lebanon tallafin Euro miliyan 60

Ministar ta shaida wa Firaministan Lebanon Najib Mikati cewa Jamus ta damu matuka kan halin da ake ciki a Lebanon kamar yadda kasar ke fadi tashin wanzar da zaman lafiya.

Karin bayani: Hezbollah ta ci alwashin daukar fansa kan Israila 

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da cewa mutane sama da 800,000 na tsananin bukatar agajin jinkai. Kazalika, akwai kimanin 'yan gudun hijrar kasar Siriya da ke jibge a Lebanon kimanin miliyan 1.2 wadanda yaki ya raba su da kasar su ta asali.