1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Ministatar wajen Jamus: Babu sulhu da Putin a kan Ukraine

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 24, 2024

Ta kara da cewa matukar aka kyale Putin ya ci karensa babu babbaka a Ukraine to babu wanda yake da tabbacin tsira daga mamaya daga Rasha

Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa

Ministatar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta yi watsi da shawarwarin yin sulhun dakatar da yakin Ukraine  da shugaban Rasha Vladmir Putin, tana mai cewar a fili take karara Mr Putin ba shi da muradin yarjejeniyar zaman lafiya.

Karin bayani:Jamus za ta ci gaba da taimakon Ukraine

Kamfanin dillancin labaran Jamus DPA ya rawaito Annalena Baerbock na shaidawa kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a Juma'ar nan a birnin New York cewa ba za su gajiya ba wajen marawa Ukraine baya, a fafutukar da take wajen kare muradanta na 'yantacciyar kasa.

Karin bayani:Jamus na da nauyin kawo karshen cin zarafi

Ta kara da cewa matukar aka kyale Putin ya ci karensa babu babbaka a Ukraine to babu wanda yake da tabbacin tsira daga mamaya daga Rasha.