1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Eurozone: Ministoci za su kare martabar Euro

December 1, 2020

Ministoci daga kasashe 19 da ke amfani da takardar kudi ta Euro sun amince a taronsu na Litinin din nan cewa za su kaddamar da gagarumin shirin kare martabar takardar kudi ta Euro.

Symbolbild Eurozone Haushalt
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Skolimowska

Tsarin da suka bullo da shi da suka yi wa lakabi da European Stability Mechanism ana sa ran zai taimaka wa kasashen Turai da kudade gami da shawarwari musamman ga kamfanoni da bankunan da zuwan annobar coronavirus ke neman durkusar da su.

A jawabin da ministan kudin Jamus Olaf Scholz yayi, ya ce tsarin zai karfafa takardar kudi ta Euro da kuma tsarin banki a nahiyar Turai. A watan gobe na Janairu ne dai ake sa ran rattaba hannu kan yarjejeniyar.