Ministocin tsaro na NATO na yin taro a birnin Brussels
February 15, 2017![James Mattis sakataran harkokin tsaron Amirka da Jens Stoltenberg babban sakataran NATO](https://static.dw.com/image/37561926_800.webp)
Talla
Ministocin kula da harkokin tsaro na NATO na yin taro a birnin Brussels na Beljiyam tare da halartar sabon sakataran harkokin tsaro na Amirka James Mattis.Ana sa ran taron zai dinke barakar da ke tsakanin kungiyar da Amirka wanda tun farko shugaba Donald Trump ya kamanta kungiyar da cewar lokacinta ya wucce.