Ministocin muhalli na taro a Nairobi
December 4, 2017Talla
Ministocin muhalli da wakilai daga sassa dabam-dabam na duniya na halartar taron da nufin tinkarar matsalar muhalli da ke sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
An kiyasta kimanin mutane miliyan bakwai ne ke mutuwa sakamakon gurbatacciyar iska. Wannan ya sa kwararru da ke halartar taron na yini uku ke ganin wajibi kasashen Afirka su tashi tsaye wajen daukar matakan dakile matsalar gurbatar yanayi a nahiyar.