1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ministocin EU na taron kakaba wa Rasha karin takunkumi

Zainab Mohammed Abubakar
July 15, 2025

Nan ba da jimawa ba kungiyar Tarayyar Turai za ta iya yanke shawara kan shirinta na kakaba wa Rasha takunkumi karo na 18.

Hoto: Yves Herman/REUTERS

Fadar Kremlin ta ce kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan da suka hada da barazanar sanya takunkumi kan masu sayen kayayyakin da Rasha ke fitarwa, suna da matukar muhimmanci kuma na bukatar nazari. Kuma Shugaba Vladimir Putin zai yi martanmi idan ya ga dacewar hakan.

A daya hannun kuma,  jami'ar kula da harkokin wajen Kungiyar tarayyar Turai Kaja Kalas, ta ce tana fatan nan ba da jimawa ba kungiyar za ta iya yanke shawara kan shirinta na kakaba wa Rasha takunkumi karo na 18.

Ministocin harkokin wajenkungiyar ta EU suna taro a birnin Brussels a yau Talata, tare da kakabawa Moscow sabbin takunkumai inda kuma, yakin da ake yi a Ukraine shi ne kan gaba a ajandar taron.

Matakin da ake shirin dauka, na ladabtarwa ya shafi bangarorin kudi da makamashi na  Rasha a matsayin martani ga kin amincewa da shugaba Putinya yi na tsagaita bude wuta a Ukraine ba tare da wani sharadi ba.