1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MINUSMA ta kawo karshen aikinta a Mali

Abdullahi Tanko Bala
December 11, 2023

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali ta kawo karshen aikinta a kasar bayan shekaru goma

Hoto: SIA KAMBOU/AFP

Shugabannin mulkin sojin Malin da suka yi juyin mulki a shekarar 2020 suka bukaci kawo karshen aikin runudunar ta Majalisar Dinkin Duniya a kasar.

Rundunar wadda aka fi sani da MINUSMA ta sassauto da tutar ta kasa a Hedikwatarta da ke Bamako babban birnin kasar Mali kamar yadda mai magana da yawun runudnar Fatoumata Kaba ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP.

An gudanar da kwarya kwaryar bikin kawo karshen aikin rundunar kiyaye zaman lafiyar.

Janye sojojin na MINUSMA dai ya haifar da fargabar za a iya cigaba da fuskantar fada tsakanin sojoji da kungiyoyi masu dauke da makamai da ke kokarin karbe ragamar ikon yankuna, Rundunar ta MINUSMA na da jami'ai 15,000 da suka hada da sojoji da yan sanda a Mali.