1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfghanistan

MMD na taro a Qatar kan makomar Afghanistan

February 18, 2024

Birnin Doha na kasar Qatar na karbar bakuncin wani taro da aka shirya karkashin inuwar Malisar Dinkin Duniya kan mokomar Afghanistan karkashin mulkin Taliban.

MMD na taro a Qatar kan makomar Afghanistan
MMD na taro a Qatar kan makomar AfghanistanHoto: Timithy A. Clary/AFP/Getty Images

Makasudin taron shine gina tubalin dawo da kasar Afghanistan cikin dangi bayan da aka mayar da ita saniyar ware tun lokacin zuwan 'yan Taliban masu kaifin kishin Islama kan madafun iko.

Sai dai da akwai rashin tabbas a game da halartar jami'an gwamnatin ta Taliban gurin taro na kwanaki biyu da ake gudanarwa a asirce.

Karin bayani: 'Yan Taliban sun gindaya sharuddan halartar taron MDD

Akalla dai jakadun Majalisar Dinkin Duniya 25 ne da karin wasu jami'ai ke halartar zaman na Doha inda za su duba yiwuwar amincewa da 'yan Taliban a matsayin halastattun hukumomin Afghanistan amma da sharadin sai sun dage takunkumin hana wa mata neman ilimi

Kasashe da dama ne dai da kungiyoyin agaji suka dakatar da bai wa Afghanistan tallafi sakamakn take hakkin dan Adam da gwamnatin Taliban mai kaifin kishin Islama ke yi tun bayan dawowarta kan mulki a shekarar 2021.