Mnangagwa ya nada sabbin ministoci
December 1, 2017Talla
Daga cikin ministocin da Mr. Mnangagwa ya nada akwai Patrick Chinamasa wanda zai jagoranci ma'aikatar kudi yayin da Major Janar Sibusiso Mayo ke a mastayin minsitan harkokin kasashen waje, shi kuwa Air Marshal Perrance Shiri a matsayin minista na kasa. Mnangagwa ya kuma maido da wasu mukarraban gwamnatin tsohon shugaban Zimbabuwe Robert Mugabe a cikin sauran mukaman gwamnati da ya nada, abin da masharhanta ke ganin ka iya haifar da kakkausar suka daga wasu 'yan kasar. A yanzu dai sabon shugaban Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa na cikin kalubalen sauya lamuran kasar musamman farfado da tattali arziki da haifar da karancin kudaden ketare da ya yi sanadiyar jefa kasar cikin mawuyacin hali.