Moden Lumana ta fice daga gwamnatin Nijar
August 22, 2013Talla
Jam'iyyar ta bayyana hakan ne a wani taron gaggawa da kwamitin kolinta ya yi dazu a birnin Yamai inda ta bayyana wannan matsayin da ta dauka.
Wakilinmu na birnin Yamai din Gazali Abdou Tassawa ya ce daga cikin dalilan da suka sanya jam'iyyar ficewa daga gwamnati akwai bayanan da su ka yi na cewar jam'iyya mai mulki na kokarin bata tafiyar jam'iyyar ta Moden Lumana.
Tuni dai jam'iyyar ta ce za yi nazari na aje makaman da ta ke rike da su sai dai wasu daga cikin 'ya'yanta na cewar ba su amince da wannan mataki da uwar jam'iyyar ta dauka.
Gabanni wannan ficewa daga gwamnatin dai, jam'iyyar ta Lumanar ta dakatar da mambobinta daga shiga gwamnatin hadin kan kasa.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mouhamadou Awal