Modi na ziyara a Ghana gabanin taron BRICS
July 2, 2025
Firaministan Indiya Narendra Modi na ziyara a Ghana gabanin taron shugabannin kasashen BRICS masu karfin tattalin arziki da za a gudanar a Brazil daga ranar 6 zuwa 7 ga watan Yulin 2025.
Karin bayani: Ghana na shirin korar dubban baki daga kasar
Firimiyan zai tattauna da takwaransa na Ghana John Mahama tare da rattaba hannu kan sabunta yarjejeniyar cinikin zinare da koko da kuma magunguna da sauran ma'adinai tsakanin kasashen biyu na kimanin dala biliyan $3.1.
Karin bayani: 'Yan Afirka za su shiga Ghana ba visa
Modi zai kasance a Ghana har zuwa ranar Alhamis, kafin daga bisani ya yada zango a kasashen Trinidad and Tobago da Argentina kafin ya isa Brazil. Akwai 'yan India sama da 15,000 da ke rayuwa a kasar Ghana, kuma wannan ce ziyarar da wani shugaban India ya kai Accra tun daga shekara ta 1995.