1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Modi ya nuna takaici kashe yara

Suleiman Babayo AMA
July 9, 2024

Firamnistan Indiya ya nuna taikacin kashe yara lokacin yaki ko hare-haren ta'addanci yayin ganawa da shugaban Rasha, kwana guda bayan harin Rasha ya halaka yara a Ukraine.

Firaminista Narenda Modi na Indiya da Shugaba Vladimir Putin na Rasha
Firaminista Narenda Modi na Indiya da Shugaba Vladimir Putin na RashaHoto: Sergei Bobylev/POOL/TASS/picture alliance/dpa

Firaminista Narenda Modi na kasar Indiya wanda yake ziyarar aiki a kasar Rasha ya shaida wa Shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha cewa kisan kananan yara na da ciwo, kulaman na firamnistan na zuwa kwana guda bayan harin da Rasha ta kai kan asibitin yara a birnin Kiev na kasar Ukraine.

Karin Bayani: Rasha ta bukaci Ukraine ta mika wuya don samun zaman lafiya

Modi ya fada haka lokacin da ake yada ganawarsa kai tsaye da Shugaba Putin a fadar Kremlin da ke birnin Moscow.

Lokacin ganawar Firaminista Modi ya fito karara ya ce kashe yara kananan a yaki, ko rikice-rikice ko kuma hare-haren ta'addanci duk abin takaici ne. Sannan jagoran na Indiya ya kara da cewa yakin ba mafita ba ne, kuma babu wata hanya illa ta tattaunawa, domin samun zaman lafiya.