1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAsiya

Mohammad Mokhber ne shugaban kasa na riko a Iran

May 20, 2024

Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sanar da mataimakin shugaban Iran Mohammad Mokhber a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya bayan rasuwar Shugaba Ebrahim Raisi a hadarin jirgin sama mai saukar ungulu.

Mohammad Mokhber ne ya zama shugaban kasa na rikon kwarya a Iran
Mohammad Mokhber ne ya zama shugaban kasa na rikon kwarya a IranHoto: Iranian Vice-Presidency/AFP

Ayatollah Khamenei ya bukaci sabon shugaban kasa Mohammad Mokhber da ya sanya ranar gudanar da zabe nan da kwanaki 50 kamar yadda yake a kundin tsarin mulkin kasar. Kazalika, an nada kwararren mai shiga tsakani kan tattaunawar Iran da kasashen yammacin duniya kan makamashin nukiliya Ali Bagheri a matsayin sabon ministan harkokin wajen kasar, wanda kafin nadin nasa shi ke rike da mukamin mataimakin ministan harkokin wajen kasar. Marigayi Raisi shi ne shugaban kasar Iran na biyu da ya mutu a kan karagar mulki, baya ga shugaba Mohammad Ali Rajai da ya mutu a 1981  sakamakon tashin wata nakiya bayan juyin juya halin Iran.

Karin bayani: Shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi ya rasu

Kasashen duniya na ci gaba da nuna alhini kan mutuwar shugaban kasar Iran Ebrahim Raisi wanda ake hasashen shi ne ke kan layi na zama jagoran addinin kasar wato magajin Ayatollah Ali Khamenei. Kantoman harkokin waje na Kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrell ya aike da sakon ta'aziyya ga daukacin al'ummar Iran bisa rasuwar shugaban kasar Ebrahim Raisi, a wani hadarin jirgin shelikwafta a jiya lahadi. Su ma shugabannin kasashen duniya ciki har da Indiya da Jamus da Amurka sun aike da sakon ta'aziyya ga gwamnati da daukacin al'ummar Iran. Kazalika kungiyar tsaro ta NATO ta nuna alhininta kan mutuwar shugaban Iran, a cewar mai magana da yawun kungiyar tsaron ta NATO.

Karin bayani: Batan dabon jirgin da ke dauke da shugaban Iran na firgita al'ummar kasar

 Shi kuwa shugaban Rasha Vladimir Putin ya sanar da shi cewa marigayi Raisi mutum ne da za a iya dogaro da shi ta kowacce fuska, a tattaunawar wayar tarho da ya yi da sabon shugaban kasar Iran na rikon kwarya Mohammad Mokhber.