1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSaudiyya

Washington: Ziyarar Mohammed Bin Salman

November 17, 2025

Yariman Saudiya mai jiran gado Mohammed bin Salman zai ziyarci Donald Trump a birnin Washington, domin tattaunawar gaba da gaba a karon farko bayan tsagaita wuta a Zirin Gaza.

Saudiyya | Riyadh | 2025 | Mohammed bin Salman | Amurka | Ziyara | Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump da yariman Saudiyya Mohammed bin SalmanHoto: Saudi Press Agency/SIPA/picture alliance

Gabanin ziyarar Yarima Mohammed bin Salman zuwa fadar White House domin ganawa da Shugaba Donald Trump, masu lura da lamuran siyasa na sa ran samun sakamako guda biyu: Sada zumunci da kuma wasu yarjejeniyoyi da aka sanya hannu. Ga Yarima Salman da ake wa lakabi da MBS dai, ziyarar na nuna cikakken komawarsa fagen siyasa a Washington. Idan ba a manta ba ziyararsa ta karshe a shekarar 2018 ta kasance mai cike da fushi dangane kisan dan jarida mai sukar Saudiyya Jamal Khashoggi, wanda ya faru a ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul da kuma aka danganta da hannun Saudiyyar.

Farfado da dangantaka?

Donald Trump da Yarima Mohammed bin Salman a taron zuba jari na kasashen biyuHoto: Saudi Press Agency/APA Images/ZUMA/dpa/picture alliance

To sai dai sannu a hankali dangantakar kasashen biyu ta fara farfadowa, lokacin da Trump ya dawo kan mulki a watan Janairun 2025. Kafarsa ta farko a ketare ita ce Riyadh, inda ya sanar da saka hannun jarin Saudiyya a Amurka na dala biliyan 600. A wannan karon a Washington, bangarorin biyu za su tattauna fasahar kirkira da hannun jari da hadin gwiwa kan batutuwan tsaro da shirin nukiliya bisa la'akari da yadda yanayin tsaro ke kara rauni a Gabas ta Tsakiya.

Karin Bayani: Sharhi: Kalaman Trump sun zama ala-ka-kai ga Yarima Salman

Neil Quilliam na Shirin Kula da Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka a Cibiyar Nazarin Dimukuradiyya ta Chatham House da ke London, ya ce bangarorin biyu za su so su gabatar da wasu yarjejeniyoyi da ke nuni da nasarar ganawara ta su. A watan Yuni Isra'ila da Amurka sun kai hari kan cibiyoyin nukiliyan Iran, wanda ya haifar da rikici na kwanaki 12. Kana a cikin  Satumba, Isra'ila ta kai hari kan shugabannin siyasa na Hamas a Qatar. Sai dai kuma a watan Oktoba an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta mai rauni da Amurka ta shiga tsakani, wanda ya dakatar da yakin kusan shekaru biyu a Gaza.

Ra'ayin masana

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

02:06

This browser does not support the video element.

A watan Satumba Trump ya gabatar da da yarjejeniyar hadin gwiwa ga Qatar, inda ya ba da tabbacin tsaron yankin Gulf bayan harin da Isra'ila ta kai wa shugabannin Hamas a Doha. Sai dai aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma ta hanyar umarnin zartarwa ba tare da gabatarwa majalisar Amurkan ba, na nufin za ta zo karshe tare da gwamnatin Trump.

Michael Stephen shi ne babban mai ba da shawa kan harkokin tsaro na Gabas ta Tsakiya a cibiyar bincike ta Royal United Services da London, ga abin da yake cewa: "Burin Riyadh samun kwanciyar hankali kuma sa Shugaba Trump ya fahimci hakan, ina ganin yana da matukar muhimmanci, kuma ko shakka babu yarjejeniyar tsaro wani bangare ne na hakan......"

Karin Bayani: Ko Iran da Amurka za su tattauna kan nukiliya?

Kafin harin da Hamas ta kai wa Isra'ila a ranar bakwai ga Oktoba 2023 da ya tayar da yakin Gaza, Isra'ila da Saudiyya suna gab da sanya hannu kan yarjejeniyar daidaita al'amura da Amurka ta jagoranta a wani bangare na yarjejeniyar Abraham. Kasashen Larabawa da suka hadar da Bahrain da Hadaddiyar Daular Larabawa da Sudan da Moroko, sun riga sun daidaita dangantakarsu da Isra'ila tun a shekarar 2020 da 2021. Ga Saudiyya yarjejeniyar za ta fi zama yarjejeniya ta bangarori uku, inda Amurka ke bayar  da tabbacin tsaro da kariya da tallafi irin wanda kasashen kungiyar NATO ke samu daga hadakar. Yarjejeniyar, za ta kuma hada da shirin nukiliya na zaman lafiya na Saudiyya.