1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Rikice-rikice

Mojtaba Khamenei ya bukaci a rufe Mashigar Hormuz

March 12, 2026

Sabon jagoran Iran Mojtaba Khamenei ya yi kira da a rufe Mashigar Hormuz domin matsa wa Amurka da Isra’ila lamba, yayin da rikicin yankin ke kara tsananta kuma farashin mai ke tashi a kasuwar duniya.

Sabon jagoran addini na Iran Mojtaba Khamenei
Sabon jagoran addini na Iran Mojtaba Khamenei Hoto: Iran state TV/AP Photo/picture alliance

A cikin jawabinsa na farko da ya fitar tun bayan da ya zama Jagoran Jamhuriyar Musulunci ta Iran, bayan mutuwar mahaifinsa Ayatollah Ali Khamenei a harin sama da Isra'ila ta kai a ranar 28 ga Fabrairu, Khamenei ya ce Iran na iya amfani da rufe mashigar a matsayin hanyar matsa lamba ga kasashen duniya.

Sabon jagoran bai bayyana fuskarsa ba a bainar jama'a ba, sai dai ya aike da jawabinsa domin mai gabatar da labarai ya karanta matsayarsa a gidan talabijin na gwamnatin Iran.

Karin bayani: Har yanzu jagoran addinin Iran bai bayyana ba

Khamenei ya kuma ce hare-hare kan kasashen yankin Gulf za su ci gaba, tare da yin alkawarin ramuwar gayya kan mutanen da suka mutu a yakin kwanaki 13 da Amurka da Isra'ila suka kaddamar kan Iran.

Isra'ila dai ta yi zargin cewa sabon jagoran Mojtaba Khamenei ya jikkata a harin da ya kashe mahaifinsa da wasu ‘yan uwansa, lamarin da ya haifar da jita-jita kan dalilin da ya sa bai bayyana a bainar jama'a ba tun da farko.