1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAfirka

Morocco ta samu tsallakawa zuwa zagaye na gaba na AFCON

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
December 30, 2025

Najeriya wadda tuni ta shiga wannan mataki na 'yan 16, a Talatar nan za ta yi wasanta na karshe a rukuni da Uganda.

Kwallon da 'dan wasan Morocco Ayoub El Kaabi ya ci Comoros da watsewa
Kwallon da 'dan wasan Morocco Ayoub El Kaabi ya ci Comoros da watsewa Hoto: Fareed Kotb/Anadolu/picture alliance

A gasar cin kofin nahiyar Afirka ta bana da ke gudana yanzu haka a kasar Morocco, an fara shiga matakin yada kanin wani, inda mai masaukin baki Morocco ta samu nasarar tsallakawa zuwa zagaye na gaba, bayan lallasa Zambia da ci 3-0 a daren Litinin.

Haka zalika Afirka ta Kudu ma ta shiga wannan zagaye na 'yan 16, bayan doke Zimbabwe da 3-2.

Sai Mali da ta tsallake rijiya da baya wajen tsallake siradi, inda ta tashi canjaras da Comoros babu ci a tsakaninsu, wato 0-0.

Karin bayani: 

Masar na sahun farko wajen shiga zagayen 'yan 16.

Najeriya wadda tuni ta shiga wannan mataki, a wannan Talata za ta yi wasanta na karshe a rukuni, inda za ta fafata da Uganda.

Sai wasa tsakanin Jamhuriyar Benin da Senegal.