1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Morocco ta fidda kasar Portugal

Binta Aliyu Zurmi
December 10, 2022

Tawagar kwallon kafa ta kasar Morocco ta yi nasarar tafiya zagayen kusa da na karshe, bayan da ta lallasa Portugal da ci daya da nema.

FIFA Fußball WM 2022 in Katar | Marokko - Portugal
Hoto: Martin Meissner/AP Photo/picture alliance

Morocco ta kasance kasa ta farko daga nahiyar Afirka da ta za ta hallarci gasar kusa dab da karshe na wasannin cin kofin duniya da ke gudana yanzu haka a Qatar.

Kasar ta Moroko dai ta yi rawar gani a wannan gasar inda kwallo daya ne ya shiga ragar ta a wasa hudu da ta buga, inda a rukunin su ta tashi da maki 7.

yanzu haka a gaba Morocco za ta kara da wanda ya yi nasara a tsakanin Ingila ko Faransa wadanda za buga nasu wasan a wannan maraicen.