Zanga-zangar kawo sauyi ta bar baya da kura a Morocco
October 1, 2025
Fiye da mutane 400 ne suka shiga hannun hukuma a Morocco, wasu sama da 300 kuma suka jikkata sakamakon tarzomar da ta barke a daren Talata a wasu manyan birane, kamar yadda ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta sanar.
'Yan tawayen Mali sun saki direbobin Morocco da suka kama
Masu aiko da rahotanni sun ce masu zanga-zangar da suka yi arangama da jami'an tsaro, na bukatar ne a gudanar da sauye-sauye a fannoni da dama ciki har da na kiwon lafiya da ilimi.
Arangamar ta fi kamari ne a yankunan Oujda da ke gabashi, da kuma Inzegane na wajen birnin Agadir a kudanci, inda masu zanga-zangar suka yi artabu da jami'an tsaro.
Morocco ta ceto 'yan cirani sama da 800
Mai magana da yawun ma'aikatar cikin gidan Morocco Rachid El Khalfi, ya ce masu boren sun yi amfani da makamai ciki har da wuka da masu da ma wasu ababen fashewa don mayar wa 'yan sandan kwantar da tarzoma martani.