Moroko ta tsare daya cikin maharan Paris
January 19, 2016Mahukunta a kasar Moroko sun bayyana cafke wani mutum dan kasar Belgium da ke da tsatso na kasar Moroko saboda alakarsa ta kai tsaye da wadanda suka kitsa kai hari a watan Nuwamba a birnin Paris.
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar ta Moroko ta bayyana cewa mutumin da aka kama shi a ranar Juma'a a birnin Al-Muhammadiya wanda ke zama kusa da gabar teku kusa da Casabalanca da Rabat nada alaka ta kai tsaye da wasu cikin wadanda suka kai harin na birnin Paris.
A jawabin da ma'aikatar ta fitar ta bayyana cewa mutumin ya yi tafiya zuwa Siriya tare da daya daga cikiin wadanda suka tashi bam da ke jikinsu a Arewacin birnin Paris a lardin Saint Denis kusa da filin wasa na kasa. Mutumin da ba a bayyana sunansa ba lokacin yana Siriya ya shiga kungiya ta Al'ka'ida reshen Al-Nusrakafin daga bisani ya kulla alaka da kungiyar IS wacce ke ikirarin kai harin na birnin Paris.