1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Morsi ya ce ya na kan gaba a Zaɓen Masar

May 25, 2012

Jam'iyar yan uwa musulmi ta ce dan takaranta na kan gaba da yawan ƙuri'u a zaɓen shugaban kasar Masar., wanda za a bayyana sakamakonsa ranar lahadi mai zuwa.

epa03086285 German Foreign Minister Guido Westerwelle (L) shakes hands with the leader of the Muslim Brotherhood's Freedom and Justice Party (FJP) Mohammed Morsi (R) in Cairo, Egypt, 30 January 2012. The FJP won the majority of the Egyptian parliament seats in the latest elections, the first ones since the ousting of former President Hosni Mubaral. Westerwelle is on a four-nation regional tour. EPA/mohamed omar
Mohammed Morsi na 'yan uwa musulmiHoto: picture-alliance/dpa

Jam'iyar 'yan uwa musulmi ta bayyana cewar ɗan takaranta Mohammed Morsi na kan gaba da yawan ƙuri'i a zaɓen shugaban kasa da ya gudana a ranukan laraba da kuma alhamis. Tun da misalin karfe tara na daren alhamis ne ake runfe runfunar zaɓe, tare da fara ƙidaya ƙuri'un a mazaɓu daban daban na ƙasar ta Masar. Sai dai hukumar da ke shirya zaɓen ba za ta bayar da sakamakon zaɓen kafin ranar lahadi mai zuwa ba. '

Yan takara 12 ne suka ƙalibalanci junansu a wanann zaɓe da ke zama na farko da aka shirya a Masar bisa tsarin demokaraɗiya, tun bayan hamɓarar da gwmnatin kama karya ta Hosni Mubarak. Ranakun 16 da kuma 17 ga watan juni ne za a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar idan ba wani ɗan takara da ya sami gagarumin rinjaye.Fiye da rabin waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a ne suka sauke nauyin da ke kansu in jin hukumar zaɓen ƙasar ta Masar.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita Yahouza Sadissou