Motsa jiki tsakanin Matasan Dosso
May 18, 2016Mai shekaru 35 ita Haoua Sani Ibrahime wadda aka ma lakabi da sunan Santia ta kasance mace ta farko da ta yi nasarar bude gidan horas da Tayekondo a Jihar Dosso, kuma ta bayyana dalilan da suka kaita da daukan wannan matakin ma'ana bude Klub
To sai dai a cewar Haoua kasancewar ta matar aure kuma a kasar da addinin musulunci ke da karfi, wasu suna wa wannan aikin nata wani kallo na daban.To amma duk da wannan matsalolin da Santia take fuskanta daga wasu mutane wannan bai hana ta samun ci gaba a cikin wannan aiki nata ba.
Kusan dai matasa maza da mata 51 ne ke samun horo a Klub din. Su dai wadannan matasan sun bayyana dalilan da ya sa su shiga wannan Klub kin don samun horo.
Ita dai Haoua ta bayyana cewar tana samun goyan baya sosei daga hukumomin jihar ta Dosso kuma yanzu haka tana shirin bube gidan motsa jiki na matan aure.