Mozambik:Afonso Dhlakama ya rasu
May 3, 2018Talla
Afonso Dhlakama dan shekaru 65 wanda ya jagoranci RENAMO sama da shekaru 30 yana yakar gwamnatin FRELOMO kafin daga baya RENAMO ta rikide ta koma jam'iyyar siyasa bayan kawo karshen yakin basasar kasar a shekara ta 1992. Za a jima ana tunawa da shi, saboda irin gudunmowar da ya ba da don samar da zaman lafiya a kasar Mozambik.