1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MUGABE DA TARON COMMOWEALTH.

November 28, 2003

ZAINAB AM ABUBAKAR.

Shugaba Robbert Mugabe na Zimbabwe yayi
barazanar ficewa daga kungiyar Common Wealth
saboda haramta masa halartan taron na
Abuja,Musamman ma Britania da wasu kasashen
farar fata da ita Engiland ta rena.Mugabe yace
lokaci yayi da Zimbabwe zatayi bankwana da
wannan kungiya domin kare mutunci da martabarta.
Zimbabwe na zargin kasashen yammaci akarkashin
jagorancin Britania da Australia da nuna
kasarsa wariya,ba domin komai ba sai domin
kwace gonakin fafaren fata da gwamnatinsa tayi
domin rabawa bakaken fatar wannan kasa.
A watan maris na shekarar data gabata aka
dakatar da zimbabwe daga kungiyar ta
Commowealth,dangane da zargin irin maguddin da
aka tabka a lokacin daya samu nasaran zarcewa
kann wannan kujera tasa.
Britani a da Australia dai sun lashi takobin
ganin cewa Mugabe bai halarci wannan taro bana
shugabannin kasashen kungiyar 54 da zai gudana
daga 5-8 ga watan Disamba a Abujan
Nigeria,ayayinda ahannu guda kuma wasu kasashen
Afrika suka nemi a barshi ya halarci taron.
A yanzu haka dai batun halarta ko kuma rashin
halartan na Mugabe shine yafi daukan hankali a
dangane da shirin gudanar da wannan taro.
A dangane da wannan batu Mugabe yayi barazanar
ficewa daga kungiyar ta common wealth,tare
dayin Allah wadan wasu shugabannin Afrika da
suka ki mara masa baya akan matakan gyaran da
gwamnatinsa tayi a dangane da raba filayen
gonaki.Yace bai ga dalilin da zaisa kasashen
yammaci kalilan da suke wannan kungiyar zasu
kasance masu jagoran alamuranta,a maimakon
bakake da sukafi yawan wakilai.
Mai shekaru 79 da haihuwa ,kuma wanda ke
shugabancin Zimbabwe tun daga samun yancin kai
daga Britania a shekarata 1980,yace masu adawa
da kasarsa dake ciki da wajen kasar sun taimaka
wajen durkusar da tattalin arzikin Zimbabwe,a
matsayin hukuncin filaye daya kwace daga
fararen fata.