Mugabe: Ina nan daram kan mukamina
November 19, 2017An dai koma kan batun tsige shugaba Robert Mugabe ne bayan da ya jadadda matsayinsa na ci gaba da jagorancin jam'iyya mai mulki a yayin da ya ke jawabi ga al'ummar kasar. Lamarin da ya yi hannun riga da sanarwar farko kan cewa Mugabe ya amince da tayin da aka masa na mika mulki cikin ruwan sanyi. Shugaban Zimbabuwen ya kuma ce zai jagoranci babban taron jam'iyyar da ake shirin yi a watan gobe duk da cewa an maye gurbinsa da korarren mataimakinsa Emmerson Mnangagwa a wani taro da aka yi a wannan Lahadin.
A jawabinsa ga 'yan kasa ya ce yana fuskantar suka daga 'ya'yan jam'iyyar da sojoji dama sauran al'umma sai dai bai tabo batun ajiye mulki ba kamar yadda aka yi tsanmani, shugaban kungiyar tsoffin sojan kasar Christopher Mutsvangwa ya fitar da sanarwa bayan jawabin Mugabe kan cewa za su shiga sabon babi na tsige shugaban da ya kwashi shekaru akalla Talatin da bakwai yana mulkin kasar a mako mai zuwa. Daman can jam'iyyar ta Zanu-PF ta bai wa Mugabe wa'adi na kwana gudu kan ya amince ya sauka daga mulki ko kuma a tsige shi.Yanzu dai za a iya cewa kallo ya koma sama a ja-in-ja da ake yi kan shugabancin Zimbabuwe a kokarin tilastawa shugaban kan mika mulki sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Larabar da ta gabata, tare da yi masa daurin talala.
Idan za a iya tunawa dai sojojin da suka karbe iko a Harare babban birnin da shugabannin coci da masu shiga tsakanin na SADC sun shafe kwanaki suna lallaba Robert Mugabe don ya sauka cikin ruwan sanyi, amma kuma yayi kunnen kashi. Mai shekaru 93 da haihuwar, bai taba fadawa cikin garari irin na 'yan kwanakin nan ba tun bayan da ya dare kan karagar mulki. Shi dai Robert Mugabe wanda aka juya babinsa a Zimbabuwe ya kasance shugaba mafi yawan shekaru a duniya.