Mugabe ya fara sabon wa'adin mulki
August 22, 2013Talla
Kamar yadda ya saba a jawabansa, Mugabe mai shekaru 89 da kuma zai yi wa'adi na bakwai a jere, yayi suka da kakkausan lafazi ga kasashen yamma da ke masa kallon dan kama karya da ma dai kasashen da ke zarginsa da tafka magudi yayin zaben da suka fafata da tsohon Firaminista kuma dan jam'iyar adawa ta MDC, Morgan Tsavangirai.