Tsohon shugaban kasar Najeriya ya rasu
July 14, 2025
Makonnin baya-bayan nan Buhari ya isa a London domin jinya, iyalan tsohon shugaban kasar sun sanar da rasuwar sa da yammacin Lahadi (13.07.2025) a wani asibiti a Landan, Garba Shehu, wanda ya rike mukamin mai magana da yawun Buhari a lokacin mulkinsa, ya bayyana a wani sako da ya wallafa a shafukan sada zumunta.
Tuni dai shugaban Najeriyar Bola Tinubu dai ya umarci sauke tuta domin alhinin rashin da kuma tura mataimakinsa zuwa birnin London domin rakiyar gawar a fadar kakakin fadar Abdul Aziz Abdul Aziz.
Sau biyu dai ana zaben marigayin domin shugabantar tarayyar Najeriyar a tsakanin shekara ta 2015 ya zuwa 2023, ko bayan mulkin soja na watanni 20 a tsakanin watan janairun 1984 ya zuwa Agustan shekara ta 1985.
Marigayin ya bar yaya 10 daga matansa guda biyu, Safinatu Yusuf wadda suka rabu a baya da kuma Aisha Halilu wadda aka fi sani da Aisha Buhari wadda ita ce za ta yi masa takaba.