Muhawarar amfani da shafukan sada zumunta
February 25, 2026
Jamusawa na ci gaba da diga ayar tambaya kan matakin gwamnatin kasar na hana yara 'yan kasa da shekaru 15 amfani da shafukan sada zumunta na intanet, bayan da irin wannan matakin ya tayar da kura a wasu kasashe da dama na nahiyar Turai. Jam'iyyar CDU mai mulkin Jamus na son a sanya iyakar shekaru 16 domin kare kananan yara, to amma kuma wasu kungiyoyi na ganin cewa ilimantar da yara kan amfani da fasahar zamani ya fi haramta musu ita gaba daya.
Kalmar cin zarafi ta intanet wato cyberintimidation, yada labaran karya maras digi, da batun tasirin kafafen sada zumunta ga lafiyar kwakwalwa musamman ma ga matasa, duk wadannan wasu ne daga cikin dalilan da suka sa kasashe da dama ke son takaita amfani da kafafen sada zumunta ga yara da matasa masu matsakaicin shekaru.
An yi irin wannan muhawara a wasu kasashen
Tun watan Disamba 2025 kasar Australia, ta zama kasa ta farko a duniya da ta haramta wa yara masu kasa da shekaru 16 amfani da shafukan sada zumunta kamar Instagram TikTok Facebook, Snapchat da X.
Matakin ya samu yabo daga wasu masu na'am da irinsa amma kuma ya sha suka daga wasu 'yan fafutika, a Faransa ma dai ana shirin haramta wa yara 'yan kasa da shekaru 15 shiga kafafen sada zumunta.
A Jamus kuwa batun na nan a matakin muhawara, Jam’iyyar CDU na tunanin shata iyakar shekaru 16 a matsayin matakin da ya cancanta, wanda ta sa firaministan kasar, Friedrich Merz, ya fara tattauna batun, bayan da ya bayyana goyon bayansa ga haramta kafafen sada zumunta ga yara kanana.
Babban dalilin da ake bayarwa a Jamus, Faransa ko Ostiraliya shi ne kare lafiyar kwakwalwar yara manyan gobe.
Abin da masana ke gani
Masana sun yi ittifakin cewa kafafen sada zumunta na kara tsananta damuwa, musamman idan aka shafe lokaci mai tsawo ana amfani da su. Ga matasa kuwa, tasirin hakan ya fi karfi, domin kwakwalwarsu na cikin matakin girma da sauyin a cikin hanzari.
Masana na ta'allaka batun da cewar tsarin wadannan kafafe na sada zumunta masu jan hankali ta hanyar "likes" da Komment ko sakonni marasa karewa na sauya yadda kwakwalwa ke sarrafa kanta zuwa girma, inda suke cewa hulda da yanar gizo na sa samu wani nishadi da jin dadi, wanda ke kara ba wa mutum sha’awar sake amfani da kafafen.
A lokacin balaga, kwakwalwa na ci gaba da girma, kuma matasa kan fi saurin neman jin dadi na gaggawa. Wani bangare na sassan jiki musamman ma kwakwalwa da ke sarrafa dabi'a da hana mutum yin abin da bai dace ba, ba ya kammala girma sai kusan tsakiyar shekaru ashirin. Wannan ne ya sa kafafen sada zumunta ke tasiri ga matasa kamar yadda kwayoyi masu sa maye ke yi masu ta'ammali da su.
Kamfanonin ba su jahilci wannan ba, shi ya sa suke mayar da hankali sosai kan matasa ta hanyar amfani da manhajojin lissafi da bidiyoyi gajeru masu jan hankali.
Sai dai kuma, domin kare yara daga illolin kafafen sada zumunta, akwai wasu hanyoyi masu tsaro Wadannan su ne kafafen da aka kerawa na musamman domin koyarwa, cikin yanayi mafi tsafta da amintacce.