1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan filayen noma gabannin zaɓen Kenya

February 26, 2013

A yayinda zaɓen Kenya ke ƙaratowa hankula sun karkata kan wanda zai samar wa talakawa filayen noma ta yadda za su sami tabbacin tsaro ta fuskar abinci

Kenya's Prime Minister Raila Odinga (C) waves alongside his Coalititon for Restoration of Democracy (CORD) alliance partners, his running mate Kalonzo Musyoka (L) of Wiper Democratic movement party and Moses Wetangula (R) of Ford party during a political rally in the coastal town of Malindi on February 9, 2013. Odinga, the presidential candidate for Coalition for Reforms and Democracy (CORD) and his running mate Kalonzo Musyoka campaigned in Mombasa and along Kenya's coast over the weekend in the build up to Kenya's general elections slated to be held on March 4, 2013. AFP PHOTO/ Will BOASE (Photo credit should read Will Boase/AFP/Getty Images)
Raila Odinga da jamiyyarsa ta CORDHoto: Will Boase/AFP/Getty Images

Shekaru shidan da suka gabata ƙasar Kenya ta gudanar da zaɓen shugaban kasa wanda ya yi sanadiyar hasaran rayuka da kuma kadarori a sakamakon rikicin siyasa da ya kunno kai.

Al'ummar kasar Kenya sun mayar da martani dangane da muhawarar da 'yan takarar neman shugabancin ƙasar Kenya suka tafka na bayyana manufofin su ga al'ummar kasar domin tantance wa ya cancanci a baiwa jagorancin kasar, a zaben shugaban kasa da ake shirin gudanarwa ranar Hudu ga watan Maris na wannan shekara.

Ƙasar Kenya da ta gudanar da zabe a shekaru shidan da suka gabata wanda ya haifar da rikice-rikice a sassa daban - daban na ƙasar, abinda daga baya kuma faɗace faɗace na ƙabilanci kuma ya ƙara dagula lamari kuma ya haifar da mummunar sakamako ga al'ummar wannan kasa .

Daya daga cikin abubuwan da suka fi daukar hankali a muhawarar bana shi ne batun mallakar filaye kamar yadda Mupa Khalfan 'yar kasar ta yi bayani

Hoto: CC-BY-SA-cimmyt

"Daya daga cikin abubuwan da ya fi daukar hankali a muhawarar shi ne batun malakar filaye.Kuma a ra'ayi na a bayane yake zagaye.-zagaye kawai shuwagabanin suka sura suna yi,suna nan suka zargin juna .wannan shi ke nuna mana cewa ba haddin kai a tsakanin shuwagabanin mu kuma sun kasa".

Mallakar filaye a Kenya

Rikicin mallakar filaye da ya ki ci yaki cinyewa a kasar ya yi sanadiyyar asaran rayuka da dama inda a karshe al'ummar kasar suka fara zargin 'yan siyasa da hannu dumu dumu a cikin fadar kabilancin kasar da cewa su ne suke zuga magoya bayan su suna kashe wasu kabilu. Francis Ouma dake zama dan kasar ta Kenya yayi tsokaci akan matsalar...

"Muhawarar ta bayyana wa duniya cewa kasar kenya ta kasa kuma tayi rauni a fanin siyasa da kuma shuwagabani.an tambayi daya daga cikin su batun filayen da yake malaka ,ya saura yana kame-kame.a bayyane yake cewa 'yan siyasar kasar Kanya makaryata ne kuma suna kai wa juna hare don haka ko daya daga cikin su bai cancanci ya zama shugaban kasa ba"

Gudunmawar Uhuru Kenyatta

Sai dai kuma a lokacin da aka yiwa dan tsohon shugaban kasar, kana dan takarar shugaban kasa Uhuru Kenyatta tambaya game da girman filin da suka mallaka? Wani dan kasar daya kalli muhawar, ya bayyana takaicin rashin samun amsar tambayar:

Uhuru Kenyatta da magoya bayansaHoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

"Uhuru Kenyatta bai bada takamaiman amsa ba,ya yi bataun falin su na Tiata Taveta kadai amma mun san suna malakar filaye da damaa da ya fi hakan, kuma cewa da yayi sun saye falayen ne yada doka ta tanadar karyane. mahaifin sa tsohon shugaban kasa ne kuma bashi da arzikin sayr mayan filaye kamar hakan".

Duk da irin rikice rikice na kabilanci da wannan kasa take fama da su ga dai bayanin tsohon shugaban kasar Mozambik Joachim Chisano a matsayinsa na shugaban tawagar sa ido akan zaben Kenya, inda ya bayyana farin cikinsa game da irin shirye shiryen da hukumar zaben kasar ta yi, bisa la'akari da abubuwan da ya gane wa idanuwarsa a zaben shekara ta 2007.

Mawallafiya: Mariam Mohammed Sissy
Edita: Saleh Umar Saleh