1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Muhawara kan fitar da ma'adanan Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
February 23, 2026

Jamhuriyar Nijar ana wata sabuwar muhawara tun bayan da babban Darectan kamfanin kula da hakar karfen Uranium na kasar Faransa na ORANO ya ambata cewa da shirye kamfaninsa yake ya zauna domin tattaunawa da kasar.

Hakar ma'adanai a Jamhuriyar Nijar
Hakar ma'adanai a Jamhuriyar NijarHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

A Jamhuriyar Nijar wata sabuwar muhawara ce ta barke tun bayan da babban Darectan kamfanin kula da hakar karfen Uranium na kasar Faransa na ORANO ya ambata cewa da shirye kamfaninsa yake ya zauna domin tattaunawa da kasar Nijar, inda a halin yanzu ra'ayoyi suka bambamta kan wannnan batu.

Abin da ya biyo baya

Kamfanin hakar ma'adanai a Jamhuriyar NijarHoto: Joerg Boethling/IMAGO

Duk da cewa dai gamnatin ta Nijar bata ce uffan kan kalaman da babban Darektan kamfanin na ORANO ya yi na cewa da a shirye suke su hau kan teburin tattaunawa da kasar ta Nijar, wannan batu dai ya bude fagen muhawara a tsakanin al'ummar kasar ta Nijar da ma makwabta inda kowa ke tofa nashi albarkacin baki.

Sai dai daga nashi bangare Inoussa Dodo Hambali, na kungiyar da ke sa ido na ganin arzikin Nijar na kalkashin kasa ya amfani ‘yan kasa, ya ce ko da suka ji kalaman shugaban Orano, sun san za a rina domin kowa na bukatar kowa.

Taka tsantsan

Hakar ma'adanai a Jamhuriyar NijarHoto: Maurice Ascani/Areva/AP Photo/picture alliance

Tuni wasu yan kasar ta Nijar ke ganin cewa dole ne fa kasarta Nijar ta yi hattara don gudun fadawa ga tarko da take neman ketarewa na kasar Faransa,  ko ma da yake a cewar Farfesa Dicko Abdourahamane mai sharhi kan al'amuran siyasar duniya, na ganin cewa tunanin samu jini ga naman fara yaudarar kai ne kawai.

Abun jira a gani dai shi ne ko hukumomin na Nijar za sukarbi abin. Da ke a tamkar tayin tattaunawa daga kamfanin na Faransa, duk da cewa bangarorin biyu na shirin wata babbar fafatawa a gaban kotu dangane da tuhume-tuhume da dama da kowa ke yi wa kowa.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani