1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan sabbin dokokin ta'addanci a Kamaru

Umaru AliyuDecember 4, 2014

Yayin da gwamnatin Kamaru ke kan samar da hukunci mai tsauri kan 'yan ta'adda da masu boye su, 'yan adawa a majalisar dama masu fafutukar kare hakki na caccakar shirin.

Kamerun Soldaten gegen Boko Haram
Farautar 'yan ta'addan Boko HaramHoto: Reinnier KAZE/AFP/Getty Images

Masu sukar wannan kuduri na gwamnati dai na fargaba ne kan yiwuwar gwamnatin kasar ta yi amfani da dokar wajen muzgunawa wadanda ke adawa da ita.

Kudurin dokar ta 3 karamin sashe na 2 kan turjiya ga ayyukan ta'addanaci a Kamaru dai yanzu na gaban majalisun kasar, wanda a ciki aka zayyana hukunci mai tsanani ga duk wani da aka kama da aikata ta'addanci, koma wanda ya hada kai da masu aikatawa a kasar.

Sai dai kamar yadda ta bayyana yanzu da dama na ganin matakin da aka shirya daukan zai take hakkin bani Adama, inda tuni ma wani dan majalisar dattatwan kasar Senata Abubakar Chiroma yace yin hakan ya saba da abin da gwamnatin Kamarun ta ki yarda shi a baya, da ma hakki na yan kasa.

Senata Abubakar Chiroma ya ce abin da mamaki ganin yadda wasu ke kokarin marawa wannan tsohuwar dokar. Lallai muna sane da batun na ta'addanci, sai dai da mamaki gwamnati ce da kanta take son kawo dokar da tafi ta'addancin tsanani. Ya kamata su girmama kundin mulkin kasa.

Baya ma ga wasu yan siyasan dake ganin rashin dacewar wannan yunkuri na gwamnati, Mr. Eugene Ngalim dake fafutukar kare hakkin jama'a a Kamaru din, na ganin wannan hukuncin kisa da kasar ke shirin dauka hukunci ne da duniyar demokuradiyya ta yi adabo da shi, kuma yin hakan a ganin sa nuna kama karya kenan.

Tsohon 'yan Boko Haram a makarantun KamaruHoto: KAZE/AFP/Getty Images

Wannan doka tana da hatsari ga yan kasar nan, saboda ana iya amfani da ita don muzgunawa wadanda ke adawa da gwamnati mai ci. Hakan kun sani zai ci karo da yancin tofa albarkacin baki na demokuradiyya, da walwala dama wasunsu.

Amma fa akwai wadanda ke ganin samar da wannan doka babu laifi a cikin sa, muddin zata hukunta yan ta'adda. Mathew Gui Eli shi ne mai wannan ra'ayi.

Muna iya cewa mataki ne mai kyau, sai dai ba kashe su ya kamata a yi kai tsaye ba, a rika ajiye su don tatsar bayanan da zasu taimaka a kawo kwanciyar hankali daga garesu.