1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan kai El Zakzaky neman magani

Uwais Abubakar Idris GAT
August 6, 2019

A Najeriya bayan da hukumar tsaro ta farin kaya ta ba da izinin tafiya da Sheik El-Zakzaky neman magani Indiya yanzu haka muhawara ta kaure a game da sharudda da kuma ka'idojin aiwatar da wannan shiri.

Nigeria Demo für die Freilassung von Ibraheem Zakzaky
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

A yayinda hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya ta sanar da aiki da umurnin kotu da ta ba da izinin tafiya kasar Indiya don neman magani ga Shugaban Kungiyar ‘yan Shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, yanayin da za’a tafi da shi kasar bisa rakiyar jami’an tsaro a yanayin na diplomasiyar kasa da kasa da ma hallacin yin haka na zama abin dubawa. 

Irin yadda hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriyar ta yi maza wajen sanar da cewa za ta mutunta umurnin kotu a kan ba da izini ko beli na tafiya neman magani ga shugaban na ‘yan Shi’a Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa ya jefa kyakkyawan fata na fara samun sauyi a kan wannan batu da ke daukar hankali sosai. To sai dai sharuddan da ta gindaya bisa cewa jami’an tsaro ne  zasu yi mashi rakiya zuwa kasar Indiya ya sanya tambayar ko akwai wannan bisda tari na diplomasiyar kasa da kasa. 

Duk da cewa har yanzu akwai abubuwa da dama da suke lullube a kan wannan batu, domin babu cikakken bayani shin wanene zai daukin nauyin kudin kai shi asibitin  a wannan yanayi da ake ciki. Akwai batu na bisa tsari na tsaron kasa da kasa, ko a tsari na ma’aikatar leken asiri akwai wannan?

Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Giginyu

Na yi kokarin jin ta bakin ofsihin jakadanci kasar Indiya a Najeriya wadanda sune za su ba da takardar izinin tafiya kasarsu, da ma hukumar tsaro ta farin kaya wacce ta bayyana mutunta umurnin kotu amma abin ya faskara.

Wannan ne dai karon farko da Najeriya ta mutumta hukuncin kotu a kan Sheikh Ibrahim Elzakzaky tun daga 2015 da ake tsare da shi, abin da masharhanta ke cewa zai yi tasiri sosai wajen sulhunta wannan batu, wanda bayanai suka tabbatar cewa sarakunan gargajiya da wasu tsaffin shugabanin Najeriya sun kai ga sa baki. Za a sa ido a ga yadda za ta kaya a kan batun.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani