1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Muhawara kan tsaro da zabe a arewa maso gabacin Najeriya

April 11, 2014

Akwai alamun rikidewar rikicin tsaron arewa maso gabashin kasar zuwa ga siyasa, inda tuni yan siyasar kasar suka fara maida martani ga bukatar a zabukan a yankin badi.

Nigeria Soldaten
Hoto: Quentin Leboucher/AFP/Getty Images

A wani abun dake zaman alamun rikidewar rikicin tsaron arewa maso gabashin kasar zuwa ga siyasa, tuni wasu masu ruwa da tsaki da siyasar kasar suka fara maida martani ga bukatar jihohin yankin uku na tabbatar da zabukan kasar na badi a cikinsu.

Sannu a hankali dai batun tsaro da zaman lafiya a yankin arewa maso gabashin Tarrayar Najeriya, sannu a hankali kuma banbancin dake tsakanin manyan jam'iyyun kasar biyu na dada nuna kansa cikin rikicin da ke cikin shekarar sa ta hudu da kuma yai sanadin asarar dubban rayukan al'umman kasar ta Najeriya. Wata sanarwar hadin gwiwar jihohi uku dake karkashin tsaro da kuma dukkaninsu ke zaman na 'ya'ya ga jam'iyyar APC dai ya nemi hukumar zaben kasar ta INEC da ta yi koyi da 'yar uwarta dake Afghanistan da ta kai ga gudanar da zabukan a daukacin kasar duk da jerin tashe tashen hankalin da ya mamaye kasar.

Jihohin na Borno da Yobe da kuma Adamawa dai sunce ba wata hujjar amfani da halin rashin tsaron da yankunan nasu ke cikin da nufin gabatar da karatun kila wakala bisa zabukan tarrayar da hukumar ke shirin gudanarwa a badi. Tuni dai daya a cikin ukun da ta kai ga gudanar da zaben a matakan kananan hukumomin jiharta ba tare da kisan kuda ba, ta zamo ma'auni ga jihohin dake fadin da biyu ga kokarin kiran ruwa da nufin kisan dan tsuntsu.

To sai dai kuma tun ba a kai ga ko'ina ba dai, matsayin na su ya fara kaiwa ga martani daga 'ya'yan jam'iyar PDP mai mulkin kasar da ke kallon jihohin uku da kokarin wuce makadi da rawa. Abun kuma da a fadar tsohon gwamnan jihar Kano, Mallam Ibrahim Shkarau, kuma sabuwar amaryar PDP a Kano bai zo dai dai da tunanin yan zaben kasar ta Najeriya ba

“ Hukumar zabe ba cewa tayi ba za'a yi zabe a Borno da Yobe dama Adamawa ba. Cewa tayi in lokacin zabe yazo yanayi bai bada dama ba bisa shawarwarin jami'an tsaro ba za'a yi zabe ba. To ka ga zancen kazo kace lallai ayi zabe ko ba za a yi ba bai ma taso ba . Sai a bari in lokaci yazo sai ayi amfani da wannan yanayi sai a ga wane irin yanayi da rahoto aka samu a Yobe suka yi zaben kanana hukumomi”.

To sai dai ko bayan jihar Yobe da,i jihohin uku sun kuma kai ga ambato zaben kasar Afghanistan a matsayin abun koyin 'yan zaben kasar ta Najeriya ga kasar da ta kai ga gudanar da zabukan al'umma duk da tashe tashen hankalin al'ummarta. Misalin kuma da daga dukkan alamu ya kasa burge tsohon gwamnan da cibiyarsa ke yankin ta arewa maso gabas, amma yace hada abun da ke faruwa a yankin da ma dan uwansa da ke Afganistan na kama da kokari na hadin sararin sama da karkashin kasa da zummar cika burin son rai.

Hoto: DW/U. Musa

“Ina ganin ai kowane yanayi da irin alkalumansa. Cewar anyi zabe a Afghanistan duk da irin wannan matsaloli ai Afghanistan shekara wajen goma sha suna abu daya. Ba lalle bane don ance yau ga wani yanayi a wani yanki a Najeriya ace sai lallai anyi zabe. Kar a manta a jihar Kaduna ba'ayi zabe da su ba a shekara ta 2011 sai daga baya saboda yanayin tsaro. Saboda haka ba wani sabon abu bane. Ni ra'ayi na shine in zabe yazo to hukumar zabe ta nemi shawarar jami'an tsaro. In sun bada tabbacin cewar babu wata matsala sai aje ai zabe amma in sunce akwai tsoratarwa ga rayuka da zaman lafiyar mutane to ai ba wani abun kuzo ku gani bane in a daga zaben nan ko a wani yanki ko karamar hukuma ko jiha. Jama'a ake yiwa, kuma ina amfani saboda kana da wata sha'awa kayi abun da zai zo ya cutar da mutane kuma”

Siyasa da rayukan al'umma ko kuma kokari na dakile tasiri na adawa dai, kace-nace na zabukan jihar dai na dada kunno kai ne kasa da tsawon mako guda da karewar wa'adin dokar ta bacin da gwamnatin kasar ta kafa, dokar kuma da jihohin sukace ba ta da amfani kuma basu son sake ganin irinta tsakanin al'ummarsu. Tuni dai wasu dattawan yankin biyu suka nemi mahukuntan yankin da ware tsabar kudi har naira miliyan dubu 600 cikin wasu shekaru biyar masu zuwa da nufin sake farfado da tattalin arziki da rayuwar al'ummar yankin da ke zaman na baya ga dangi a daukacin kasar.

Mawallafi: Ubale Musa
Edita: Umaru Aliyu