1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Muhawara kan yawan albashin majalisar riko

Gazali Abdou Tasawa ZMA
June 30, 2025

Sabon cece-kuce ya taso, a game da yawan kudaden albashin da doka ta ware wa mambobin majalisar mashawartar rikon kwarya ta kasa wacce aka kaddamar a karshen mako.

Hoto: Boureima Hama/AFP/Getty Images

Kazalika wasu ‘yan kasar na nuna damuwa game da adadin yawan ‘yan majalisar kusan 200 da kuma kudaden da za su lakume a daidai loakcin da kasar ke fama da matsalolin kudi a yayin da kuma akasarin talakawa kasar ke rayuwa irin ta ‘yan rabbana ka wadata mu. Sai dai ‘yan majalisar da dama na cewa kudaden da aka ba su, basu taka kara sun karya ba idan aka kwatamta da kudaden da suke samu a ayyukansu na asali.

Sabuwar dokar kudaden albashi ko kuma alawus na 'yan majaslisar shawara ta kasar ta Nijar dai ta tanadi kudi kaso dabam-dabam tsakanin masu mukami da kuma marasa mukami a cikin majalisar. A jimulce dai ko-wane dan majalisa da ba shi da wani mukami na da albashin jaka 365 da 'yan kai a ko-wane wata. Sannan zai a dinga biyan kowanensu jaka 50 a ko-wace rana a loakcin zaman majalisar, ya kasance zama na al'ada wato session ordinaire ko kuma na gaggawa wato session extraordinaire. Kuma gwamnati ke daukar nayin kaso 80 cikin dari na kula da lafiyar dan majalisar da iyalinsa.

Daga nashi bangare, shugaban majalisar da sauran mambobi 26 masu rike da mukamai za su dinga samun albashinsu ne a ko-wane wata. Kuma shugaban majalisar ke da biya mafi tsoka na sama da miliyan biyu da jika 297 na CFA a ko-wane wata da suka hada da kudin haya da na wuta da ruwa da tarho da dai sauran dawainiya na aiki da kuma gida. A yayin da sauran na kasa da shi ke da albashin da ya tashi daga jaka 705 zuwa  miliyan daya da jika 296. To sai dai tuni wasu ‘yan kasar suka soma nuna damuwarsu da girman albashin ‘yan majalisar da ma adadin mambobinta.

To sai dai wasu daga cikin mambobin majalisar na ganin kudin albashin nasu bai taka kara ya karya ba idan aka yi la'akari da ayyukan da suka sadaukar domin yin wannan aiki. Ko ma dai wane irin albashi ne 'yan majalisar shawarar ta gwamnatin rikon kwaryar kasar ta Nijar za su dauka, ‘yan kasa sun zura musu ido su ga tasirin da ayyukan da za su yi a majalisar za su yi wajen ciyar da kasar a gaba.