1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Touadera: Turai ta janyo gudun hijira

September 21, 2023

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin Archange Touadera, ya zargi kasashen yammacin duniya da haddasa 'yan gudun hijira sakamakon mulkin mallaka da cinikin bayi da mamaye arzikin nahiyar Afirka da suka yi.

Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera
Shugaban Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya Faustin-Archange TouaderaHoto: BRENDAN MCDERMID/REUTERS

Shugaba Touadera na jawabi ne game da tururuwar da 'yan gudun hijirar daga Afirka suka yi a Tsibirin Lampedusa na kasar Italiya, lamarin ya sha kan jami'an da ke kula da su, har ma Kungiyar Tarayyar Turai ta fara nuna damuwa a kai. Ya kara da cewa kwararar bakin hauren na nuni da irin mawuyacin halin da al'ummar Afirka ke ciki, ta dalilin mulkin mallaka da Turawan suka yi wa nahiyar, inda suka kakaba wa al'umma fatara da talauci ta'addanci marar misaltuwa. Jawabin nasa na zama martani ga jawabin da Frimainistan ItaliyaGeogia Meloni ta yi a jiya Laraba, tana sukar lamirin safara mutane daga Afirka zuwa Turai don neman ingantacciyar rayuwa.