Mulkin mulka'u a Kamaru ya ja hankali a Jamus
August 29, 2025
Za mu fara da Jaridar Die Zeit wadda ta yi sharhinta a kan zaben shugaban kasa a kasar Kamaru.
Jaridar ta ce shugaban kasar Kamaru Paul Biya shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya. A shekarunsa 92 yana shirin sake tsayawa takara a karo na takwas. Sai dai matasan kasar sun ce sun gaji da mulkin tsofaffi.
A Kamaru ana jin amon dimukuradiyya ne kawai a takarda to sai dai hakan ba zai dore ba a cewar Adeline Tsopgni wata matashiya duk da ta san furta irin wannan ra'ayi yana da hadari a cikin Kamaru. An haramta yin duk wani hasashe game da lafiyar shugaban kasar tun 2024. A wancan lokaci shugaban ya yi tafiya zuwa kasar Switzerland tsawon makonni. A gida an yi ta yada zita-zitar cewa ya rasu amma bai mutu ba. Gidan talabijin din kasar ya sanar da dawowarsa cikin kasa.
Mutane da dama a Kamaru ba su da tabbas kan shugaban nasu, suna ganinsa ne kawai a jawabin sabuwar shekara ko hutu na kasa baki daya. Rabon kuwa da ya yi taron majalisar gudanarwar gwamnati tun shekarar 2019. Ba boyayyen abu ba ne cewa Biya zai sake tsayawa takara saboda tsarin bai fitar da wanda zai gaje shi ba. Ko su kansu mukarabbai na hannun damansa shekaru sun cimma su domin kuwa sun haura shekaru 80. Mulki ne dai na tsofaffi wadanda ba sa son gusawa.
Gwagwarmayar tsofaffi ta ci gaba da rike madafun iko ba a Kamaru kawai ta ke kara kamari ba, matsalar na neman mamaye dukkan Afirka. Babu wata nahiya a duniya da yawan al'umarta matasa ne da shekarun su ya kama daga 19, haka kuma babu wata nahiya da tsofaffi suka yi babakere a kan mulki irin Afrika domin kuwa a wadancan nahiyoyi yan kadan ne cikin masu hankoron neman mulkin da suka haura shekaru 80.
Jaridar die tageszeitung ta yi na ta sharhinta ne a kan mace macen da ke faruwa a Sudan. Inda ta ce yakin Sudan na kara jefa al'umma cikin ukuba da tagaiyyara. Musamman a yankin Darfur inda mayakan sa kai na RSF suke iko. Birnin kasuwanci na El Fasher kuma babban birnin arewacin Darfur yanzu ya zama matattarar yunwa.
Tun barkewar yakin Sudan lokacin da rundunar sa kai ta RSF ta ke cikin sojojin gwamnati ta fara ta tayar da kayar baya a tsakiyar watan Afrilun 2023, Darfur ta ga bala'i mafi muni. Shugaban RSF Mohammed Hamdan Daglo wanda aka fi sani da Hameti ya taho daga Nyala a kudancin Darfur inda ya ayyana birnin a matsayin cibiyar gwamnatinsa ta aware wanda ya kara jaddadawa yan makonni da suka wuce.
Cikin watanni 18 da suka wuce RSF ta kai hare hare sansanoni da dama na yan gudun hijira. A ranar 11 ga watan Afrilu RSF ta kai hari sansanin yan gudun hijira mafi girma a El Fasher wato sansanin Zamzam inda ta tilasta wa mutane 500,000 daga cikin mutum 800,000 da ke sansanin tserewa. Da dama daga cikin yan gudun hijirar sun galabaita bayan shafe tsawon makonni suna tafiya cikin hamada babu abinci ko ruwa inda suka samu suka isa garin Tawila mai tazarar kilomita 60. Asusun kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta koka cewa mutane na fama da yunwa da kishin ruwa.Majalisar Dinkin Duniya ta ce fadan da ake yi a kusa da El Fasher ya yunwa ta tsananta a yankin a cikin wannan watan na Augusta.
A sharhinta mai taken gwagwarmayar neman Angizo, Japan na ja da China wajen samun tasiri a Afirka ta hanyar zuba jari da ayyukan raya kasa.
Jaridar ta ce taron da aka gudanar a birnin Yokohama na Japan mai tashar jiragen ruwa, ka ce tamkar taro ne na kungiyar gamaiyar Afirka. Kusan wakilan daukacin kasashen sun halarta inda suka yi hoto da Firaministan Japan Shigeru Ishiba da kuma Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres.
Muhimmancin taron kuma abin da ya fito fili shi ne gogayyar samun albarkatun Afrika. Japan na iya cike gurbin da Amurka da Turai suka bari na raunin zuba Jari a cewar Asuka Tatebayashi wani masanin siyasar kasa da kasa yayin da Amurka ta mayar da hankalinta a cikin gida da kuma barazanar kakaba wa kasashe karin haraji, a waje guda kuma Turai ta karkata dukiyarta don inganta tsaron nahiyarta.
Jaridar ta die tageszeitung ta ce Japan ta yi alkawarin habaka zuba Jari tare da taimakon raya kasa ga Afirka.Haka kuma za ta bai wa bankin raya kasa na Afirka rancen Dala biliyan biyar da rabi da kuma karin dala biliyan daya da rabi a harkokin gwamnati da na yan kasuwa masu zaman kansu.
Sai dai ayar tambayar ita ce ko tsarin zai dore. Sai dai abin sha'awa shi ne yadda Afrika ke daukar hankali ta fuskar tattalin arziki inda kamfanonin Japan suka karu zuwa 950 a Afirka cikin shekaru 15 da suka wuce yawancinsu kananan kamfanoni da kuma masu tasowa yayin da manyan kamfanonin sukabdan ja baya saboda fargabar hasara.