Mummunan hali na 'yan gudun hijira a Turai
June 13, 2016 Shugaban hukumar kare hakkin 'yan Adam a Majalisar Dinkin Duniya Zeid Ra'ad Al Hussein, ya koka kan yadda 'yan gudun hijira ke shan azaba a kan iyakar kasashen Girka da Italiya. Shugaban ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ake girke yara kanana a gidajen yarin da ke killace da wayoyi. Zeid Al Hussein ya kirayi hukumomi da su nemar wa yara kananan mafita a yayin da suke neman mafaka.
Zeid Ra'ad Al Hussein, ya kuma bukaci majalisar koli ta hukumar kare 'yancin dan Adam ta MDD da ta karfafa kiraye-kirayenta kan yadda ake cin zarafin 'yan gudun hijira a wasu kasashen Turai. 'Yan gudun hijirar Iraki da Siriya na jibge a kan iyakokin kasashen Turai tun bayan da EU ta cimma yarjejniya da Turkiyya, wacce ta tanadi mayar da su inda suka fito.