1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mumunar hare haren dakarun gwamnati a Siriya

May 26, 2012

A ƙalla mutane guda 50 suka mutu galibi yara ƙanana a garin Houla da ke a tsakiyar kasar ,

Syrian army soldiers and rebels sit on the top of an armored personnel carrier shortly after the Syrian soldiers defected and joined the rebels, in Khaldiyeh district, in Homs province, central Syria, Saturday May 12, 2012. Syria's uprising started in March 2011 with mostly peaceful protests inspired by successful revolts elsewhere calling for political reform. The Syrian government responded with a brutal crackdown, prompting many in the opposition to take up arms to defend themselves and attack government troops. (Foto:Fadi Zaidan/AP/dapd)
Hoto: AP

Masu aiko da rahotannin sun ce a karon farko dakarun gwamnatin sun kutsa da tankokin yaƙi a garin Alepo birni na biyu ma fi girma inda suka rika fatatakar jama'a.Babban kwamitin zataswa na ƙungiyar yan adawa ta ƙasar CNS ya buƙaci kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya gudanar da wani taron gaggawa bayan abinda ya kira kisan kiyasun da aka yi a garin na haula da ke kusa da Homs.

Wannan al'amari wanda wasu majiyoyin yan adawa suka ce ya rutsa da mutane sama da guda ɗari galibi yara ƙanana;na zuwa ne a daidai lokacin da aka shirya manzon masamman na MDD Koffi Annan zai yadda zango a ƙasar ta Siriya a makon gobe.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou