Amfani da karfi don murkushe masu zanga-zanga a Iraki
October 8, 2019Talla
Kiraye-kirayen shugaban na zuwa ne biyo bayan amincewar da rundunar sojan kasar ta Iraki ta yi na cewa ta yi amfani da karfin tuwo fiye da kima wajen tarwatsa masu boren, wadanda ke nuna rashin amincewarsu da matsalolin rashin ingancin rayuwa da rashin aikinyi, uwa uba da cin hanci da rashuwa da masu zanga-zangar ke zargin gwamnatin da aikatawa.
Masu aiko da rahotanni sun bayyana cewa bayan shafe tsawon kwanakin ana zanga-zanga, da akwai fargabar kara samun wani boren nan da 'yan kwanaki, duba da yadda mabiya darikar Shi'a ke shirin gudanar da bukukuwan Arba'in a Karbala, domin cika zagoyowar kwanaki 40 da kisan Imam Husseinwanda suke gudanarwa ko wace shekara.