Murkushe masu zanga-zanga a Brazil
June 20, 2013Gwamnatin kasar Brazil ta tura jami'an 'yan sanda na musamman zuwa sassa daban-daban na kasar da gasar kwallon kafa ta "Confederations Cup" ke gudana a yanzu haka. Tun dai a karshen mako ne dubban 'yan kasar ta Brazil su ke gudanar da zanga-zangar nuna bacin ransu kan biliyoyin kudaden da gwamnati ta kashe wajen shirya gasar ta "Confederations Cup" da kuma gasar kwallon kafa ta duniya da za a gudanar a kasar a shekara ta 2014 mai zuwa.
Masu zanga-zangar na ganin cewa kamata yayi a kashe wadannan kudade wajen inganta bangarorin Ilimi da Kiwon Lafiya. A nata bangaren shugabar kasar ta Brazil Dilma Rousseff, ta ce ta saurari koken al'umma kuma a shirye ta ke ta biya musu bukatunsu, yayin da tuni wasu gwamnatocin jihohi suka bayyana janye karin kudin ababen hawa da aka yi wanda shi ne ya tunzura masu zanga-zangar.
Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe