Shirin sulhunta Armeniya da Azerbaijan
October 10, 2022Sakataren harkokin wajen Amirka Antony Blinken ne ya shiga tsakani don ganin an yi sulhu a tsakanin Armeniya da makwabciyarta Azerbaijan da suka jima suna fada da juna, a matakin farko da ke nuna an kama hanyar sulhunta rikicin, bangarorin biyu sun amince su yi musayar fursunoni kimanin goma sha bakwai, an cimma matsayar bayan wata tattaunawa da Mista Blinken ya yi ta wayar tarho da Shugaba Ilham Aliyev na Azerbaijan a wannan Litinin.
Blinken ya kuma bayyana aniyar Amirka na ba su goyon baya wurin warware muhimman batutuwan da suka haifar da sabanin, musamman bayar da damar hawa teburin sulhu kan yankin nan na Nagorno-Karabakh da suka jima suna jayayya a kai. Rayuka fiye da dari biyu ne suka salwanta a rikicin baya-bayan nan a tsakanin makwabtan biyu.