Yuganda: Shin Museveni zai ci gaba da jagoranci?
September 23, 2025
Ga miliyoyin ‘yan Yuganda da ke kasa da shekaru 40, Yoweri Museveni shi ne shugaban kasa daya tilo da suka taba sani. Kuma a shekarunsa na haihuwa 81, Museveni na shirin fara wani sabon yakin neman a zabe shi, bayan hukumar zaɓe ta tabbatar da sunansa a jerin ‘yan takara na zaben shugaban kasa na watan Fabrairu mai zuwa.
Share tsawon shekaru kan madafun iko
Shugaban Yuganda Yoweri Museveni ya hau karagar mulki a 1986, bayan ya jagoranci juyin-juya-hali da ya kifar da gwamnatin Milton Obote.
Kimanin shekaru arba'in bayan haka, shi ne ɗaya daga cikin shugabannin da suka dade suna mulki a duniya. Mulkinsa ya sami yabo da suka.
Masu goyoon baya
Masu goyon baya na cewa Museveni ya kawo zaman lafiya bayan shekaru masu cike da rikici.
A fannin tattalin arziki, Yuganda ta sami canji. Ana noma kayan gona daban-daban, ba wai kofi ko gahawa kadai ba.
fannin yawon shakatawa ma ya karu, kasuwanci a cikin ƙasashen Gabashin Afirka ma ya bunkasa. Inda kasar ke da albarkatun mai mai yawa, kusan gangar mai biliyan shida. Asusun ba da lamuni na IMF na hasashen cewa idan aka fara hakar mai, za a samu bunƙasa mai yawa.
Amma duk da haka, har yanzu Yuganda na dogara da tallafin ƙasashen waje, A gefe guda, cin hanci da rashawa na ci gaba da zama babbar matsala.
Hukumar Kula da Harkokin Gwamnati ta kiyasta cewa kusan tiriliyan 10 na shilling na Yuganda (kimanin euro biliyan 2.4) na bacewa duk shekara saboda rashawa.
Shin akwai mafita?
Yuganda dai na samun matsayi mara kyau a bangaren bin doka da soke nauyi da alhakin gwamnati kan al‘uma. Zaɓe sau da dama a kasar na gamuwa da tashin hankali. ‘Yan takarar adawa suna fuskantar tsangwama, tsarewa, har ma da sace su.
Ko masu goyon baya ma na ganin cewa ‘yancin adawa na da iyaka a kasar. Robert Onyango matashi dan aksa da 40, ya ce ana iyakance ‘yancin siyasa a kasar, kuma hakan ba abin mamaki ba ne.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam suna gargadi kan ƙaruwar matsin lamba, duk da ci gaba da aka samu a shekarun 1990, jami’an gwamnati yanzu na amfani da iko wajen tauye ‘yancin jama’a.
Haka kuma ‘yancin ‘yan jarida ya ragu, inda ake kai hari kan wadanda ke daukar rahotannin adawa.
Duk da haka dai, Shugaba Yoweri Museveni dai bai nuna alamar yin murabus ba.