Museveni na son mulkin mutu ka raba
July 27, 2018Talla
A baya dai doka ta tsara cewa shugaban kasa ya zama wajibi ya kasance yana kasa da shekaru 75, wannan kuwa da zai iya zama karan tsaye ga Museveni da ke kan mulki tun a 1986, ya nemi a sake zabensa a shekarar 2021.
'Yan adawa dai a Yuganda sun yi fatali da shirin majalisar dokokin kasar a watan Disamba bayan da suka amince da cire ka'idar shekarun ga shugaban kasa, lamarin da ya haifar da zanga-zanga har da garzayawarsu kotu don kalubalantar matakin da a yanzu kotun ta sake jaddadawa.