Musharraf EU
January 21, 2008Talla
Kafin ganawarsu da Mr Musharraf, kafafen yaɗa labarai sun rawaito kantoman ƙungiyyar Tarayyar Turai, Mr Javier Solana na cewa, ci gaban dangantakar ƙungiyyar ta Eu da ƙasar Pakistan zai ta´allaƙa ne ga yadda aka sa halin da´a, a zaɓen gama gari da ƙasar ke shirin gudanarwa. Mr Solana ya kuma jaddada wannan batu, a lokacin ganawarsa da Mr Musharraf, yayin da suke cin abincin rana a yau ɗin nan a can birnin na Brussels. Mr Javier Solana, dake karɓar baƙuncin Mr Musharraf ya ci gaba da cewar: ´´ Mr Solana ya ce tuni muka gayawa shugaba Musharraf aniyarmu na ganin cewa an gudanar da zaɓe mai tsafta dake cike da adalci da kuma kwanciyar hankali a ƙasar. Hakan a ganin mu shi zai dasa ƙasar Pakistan a turba mai kyau da ka iya kaita izuwa tudun mun tsira´´ Da alama dai wannan gargadi na ƙungiyyar ta Tarayyar Turai ba zai rasa nasaba da yadda jam´iyyun adawa na ƙasar ke zargin Gwamnati da ƙoƙarin shirya maguɗi, a zaɓen na gama gari da ake shirin gudanarwa a watan na gobe ba. Tuni dai masu sa ido na ƙungiyyar Tarayyar Turai suka isa ƙasar ta Pakistan, don ganewa idonsu yadda Gwamnati ke shirye-shiryen gudanar da wannan zaɓe, dake ci gaba da ɗaukar hankalin Duniya. Har ilya yau, a waje ɗaya kuma ana kuma zargin Mr Musharraf da gazawa, wajen samarwa Benazir Bhutto ingantaccen tsaro, wanda hakan ya haifar da yi mata kisan gilla a ranar 27 ga watan Nuwambar Bara. Ba sau ɗaya ba sau biyu ba, Mr. Musharraf ya ce ya sha gargadin Benazir Bhutto yin taka tsan-tsan, dangane da yadda take gudanar da al´amurranta, amma a cewar shugaban tayi kunnen uwar shegu da irin wannan nasiha. Kafafen yaɗa labarai a can baya sun rawaito Mr Musharraf na zargin ´yan ta´adda da hannu a kisan tsohuwar Faraministar ta Pakistan, wato Benazir Bhutto. Shugaban na Pakistan ya ci gaba da cewar: ´´ Tuni na ruga na shaidawa sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya irin ƙudiri da jajircewar Pakistan, wajen ci gaba da yaƙi da ayyukan ´yan ta´adda da masu tsattsauran ra´ayi. Za kuma mu ci gaba da kyakkyawar dangantakar dake akwai a tsakaninmu da ƙungiyyar Eu da kuma dakarun tsaro na ISAF dake Afghanistan´´ Mr Musharraf dake rangadin ƙasashe huɗu a Nahiyar ta Turai ya shaidawa Mr Solana cewar, Pakistan na samun nasara a yaƙin da take da ayyukan ´yan ta´adda a ƙasar da kuma iyakokinta da Afghanistan. Bugu da ƙari, shugaban na Pakistan ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatinsa a shirye take ta nuna halin dattako da adalci a zaɓen gama gari, wanda jam´iyyar Benazir Bhutto ta PPP tuni ta ƙudiri aniyar shiga cikinsa. Ana kyautata zaton cewa shugaban na Pakistan na wannan rangadin ne, don neman haɗin kan ƙasashen Turai ne ga Gwamnatinsa, dake fuskantar suka a ciki da kuma wajen ƙasar. A makon da muke ciki ne, ƙungiyyar ƙasa da ƙasa dake fafutikar kare haƙƙin bil adama ta zargi Mr Musharraf da yin karan tsaye ga wasu dokoki da ka iya haifar da tsaftataccen zaɓe a ƙasar. Daga cikinsu a cewar ƙungiyyar ta FIDH, akwai yadda jami´an tsaro ke ci gaba da tsare ´yan adawa da masu fafutikar kare hakkin bil adama a ƙasar. Irin waɗannan abubuwa da ma kuma wasu na daban ya haifar ƙungiyyar ta ƙasa da ƙasa buƙatar ƙungiyyar Tarayyar Turai jan kunnen Mr Musharraf, a matsayinta na abokiyar cinikin ƙasar ta Pakistan. Har ilya yau ƙungiyyar ta FIDH ta kuma buƙaci Mr Musharraf kafa kwamiti mai zaman kansa don gudanar da bincike na musanman game da kisan gillar da akayiwa shugabar adawa ta ƙasar Benazir Bhutto.
Talla