Musharraf ya lashe zabe a Pakistan
October 6, 2007Sakamakon zaben shugaban kasa a kasar pakistan na nuni dacewa,shugaba Pervez Musharraf ya lashe wannan zaben.Duk dacewa baa sanar da sakamakon a hukumance ba,yanzu ya rage ga kotun kolin kasar zartar da hukunci adangane da ko zaa rantsar da Musharraf cikin kakin soji ko kuma akasin haka.Da wannan sakamako dai ana saran shugaban Pakistan din zai zarce na tsawon karin shekaru biyar akan mukaminsa,duk dacewa yan majalisa 160 suka yi murabus domin nuna kokensu akan wannan sakamako,ayayinda wakilan jamiiyyar tsohuwar prime ministan Benezir Bhuto suka kauracewa zaben.Idan har aka tabbatar da wannan sakamako,Musharraf yayi alkawarin cire kakin sa na soji,domin a rantsar dashi a matsayin shugaban mulkin farar hula,wanda zai auku shekaeu 8 bayan kifar da gwamnatin kasar da bakin bindiga.