Ziyarar musulmai a sansanin Auschwitz
January 23, 2020A wajen da yanzu haka ke kasar Poland masu mulkin Jamus karkashin jagorancin 'yan Nazi sun kashe kimanin Yahudawa miliyan 1.1 lokacin yakin duniya na biyu har zuwa shekarar 1945. Raed Saleh wanda yake cikin 'yan siyasa na Jamus karkashin jam'iyyar SDP a matsayin dan majalisa a shekara ta 2013 tare da matasa, sun ziyarci wannan sansanin gwale-gwalen. Duk da haka akwai karancin Larabawa daga cikin adadin maziyarta kimanin 3,200 kacal a cikin alkaluman a hukumance. Sai dai shugaban kungiyar kasashen Musulmai ta duniya Mohammed Al-Issa kana tsohon minista a gwamnatin Saudiyya ya kai ziyara sansanin tare da David Harris shugaban Yahudawa na Amirka wanda iyayensa suka tsira daga wannan azaba. Sannan shugaban kungiyar kasashen Musulmai ta duniya Mohammed Al-Issa ya bukaci daukacin Musulmai su goya daga abin da ya faru a tarihi.