1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSaudiyya

Musulmi na hawan Arfat cikin tsananin zafin rana

June 15, 2024

Alhazzai sama da miliyan guda da rabi na gudanar da hawan Arfat a wannan Asabar, sai dai a bana ana gudanar da ibadar da ke zama ginshikin aiki Hajji cikin yanayi na tsananin zafin rana.

Hawan Arfat cikin tsananin tsafin rana
Hawan Arfat cikin tsananin tsafin ranaHoto: Amr Nabil/AP/picture alliance

Tun da sanhin wannan safiya alhazzan ke ta tururruwa domin zuwa hawan dutsen na Arfat mai tsawon mita 70 wanda ke a tazarar kilomita 20 daga birnin Makka, inda a can ne manzon Allah SAW ya yi hudubarsa ta bankwana.

Alhazzan sama da miliyan guda da rabi cikin fararen tufafin harami za su share tsawon wuni guda cur suna gudanar da addu'o'i a samman dutsen mai matukar daraja kamar yadda kundin aikin Hajji ya tanadar.

Karin bayani: Azumin ranar Arfat ga musulmi

A cewar cibiyar hasashen yanayi ta Saudiyya ana sa ran zafin rana ya kai maki 43 a wannan Asabar a Arfat, sai dai amma mahukutan kasar sun yi tanade-tanade masuman ma ga tsofaffi da kuma marasa lafiya.

Bayan kammala hawan Arfat mummunai za su je Muzdalifah inda za su tsinci duwatsu don aiwatar da ibadar 'jifan shadan' a gobe Lahadi kafin su karkare da sauran ibadun aikin Hajjin.