1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Musulmi na shirin zama magajin garin London a karon farko

Suleiman BabayoMay 6, 2016

Babbar jam'iyyar Labour za ta rasa tasiri bayan zaben yankuna da kananan hukumomi a Birtaniya. Amma ta na shirin kafa tarihi inda Musulmi zai iya zama magajin garin London.

Großbritannien Wahlen Sadiq Khan
Hoto: picture alliance/ZUMAPRESS/D. Leal-Olivas

Akwai yiwuwar babbar jam'iyyar adawa ta Labour a kasar Birtaniya za ta rasa kujeru da dama da take da su a zaben yankuna da kananan hukumi da ya gudana a wannan Alhamis da ta gabata. Jam'iyyar 'yan kishin kasa ta Scotland ta yi ikirarin samun rinjaye, kuma akwai yiwuwar ta zama jam'iyya ta biyu mafi tasiri, wannan bayan jam'iyyar Labour ta mamaye siyasar yankin Scotland cikin shekaru da dama da suka gabata.

Sai duk da shan kayi akwai yiwuwar jam'iyyar adawa ta Labour ta samu nasarar kwace kujerar magajin garin birnin London fadar gwamnatin kasar daga hannun jam'iyyar mai mulki ta Conservative, inda dan takara na Labour a zaben Sadiq Khan kuri'ar jan ra'ayi ta nuna ya na kan gaba, kuma idan ya kayar da Zac Goldsmith na Conservative zai zama Musulmi na farko da ya jagoranci wannan birnin mai tasiri a yammacin kuma birnin mai karfin arziki da tasiri a duniya baki daya.

Nan gaba a wannan Jumma'a za a samu cikekken sakamakon zaben.