Musulmin duniya na gudanar da bikin Sallah layya
October 4, 2014Talla
Sama da mutane miliyan biyu ne da ke yin aikin hajji a ƙasa mai tsarki ta Saudiyya.Suka fara aikin ibada na jiffar sheɗan a garin Mina da ke kusa da Makka a yau ranar da musulmin duniya ke gudanar da bukukwan Sallah layya.
Aikin ibadar na jiffar sheɗan na ɗaya daga cikin manyan aiyyukan da suka zama wajibi ga mahajjatan bayan tsayuwar Arfa wacce aka yi a jiya. Wakilin DW a Makka Abdullahi Maidawa Kurgwi ya ce a bana ana gudanar da ibadar cikin wani yanayi na zafin rana mai tsananin gaske.