1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Musulmai a Sudan na fama da rashin buda baki

Mahmud Yaya Azare M. Ahiwa
March 29, 2024

Bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana Sudan a matsayin kasar da ke daf da tsunduma cikin yunwa sakamakon yaki, al‘ummar kasar na fafutuka kafin samun abincin buda baki.

Yadda wasu ke buda baki a Sudan
Yadda wasu ke buda baki lokacin Azumi a SudanHoto: AFP/A. Shazly

Ba kamar yadda aka saba gudanar da buda bakin Azumin Ramadhana a kasar ta Sudan da ake kakkafa runfuna a unguwanni da masallatai don yin na gayya kyauta cikin murna da annashawa ba, a wannan karon galibin manyan masallatan biranen Khartoum da Umdurman, ko dai an mayar da su kufayi ko kuma sansanonin da dakarun soji ke jan daga a cikinsu ne a yanzu.

Matasa da suka saba yin buda bakinsu a rumfunan masu sayar da shayi da Gahawa, galibinsu sun dau makamai ko dai don kare unguwanninsu daga ‘yan wasoso, ko kuma sun shiga yaki karkashin daya daga cikin bangarori masu yaki da juna, lamarin da ya sanya buda bakin a bana ya zamto na daban.

Su kansu ‘yan mata da a kwanakin karshen na Ramadhana ke yin tashen da suke samun kudin kayyakin Sallah daga yinsa, sun ce in ana ta kai ba a ta kaya, kamar yadda Khuloud Ibrahim wata matashiya ‘yar Sudan din ke fadi.

"Ramadhan din bana ya saba da wadanda muka yi tayi a shekarun baya cikin annashuwa da farin ciki. A wannan karon, mata da aka san su da sayar wa mutane shayi duk sun bace. Batun tashe da ‘yan mata ke yi babu shi. Don haka babu hanyoyin samun kudin abincin buda baki ballantana kuma a yi maganar kayan sallah. A gaskiya a yanzu muna cikin yunwa da bakin ciki da damuwa."